
Bidiyo ya bayyana dake nuna cewa, a watan Yuni an bayyana yanda aka sace karafan dake rike da titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna amma ba’a dauki mataki ba.
A jiya ne dai jirgin kasan yayi hadari inda mutane 6 suka jikkata sannan wani mutum daya ya rasu kamar yanda rahoton ya nunar.
A Bidiyon an ga yanda wani ke nuna karafan jirgin kasan a kwance babu wani karfe dake rike dasu.