
Malam Lawal Triumph ya bayyana cewa, Ahlussunah sune masoya Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) na gaskiya.
Ya bayyana hakane yayin wani wa’azi da aka yi bayan Bayyanarsa a gaban Kwamitin Shura na Kano ya kare zargin da ake masa na munana kalamai ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Malam yace duk wanda yace wani musulmi baya son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) to kamar ya kafurtashi ne dan son Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ginshiki ne a Musulunci.