
Babban yaron Nazir Ahmad Sarkin Waka, Abba C Sale yace ya janye maganar da ya taba yi a baya wadda ta jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta.
Abba ya taba cewa, yana samun Naira Miliyan 5 a wata wanda hakan yasa mutane sukaita cece-kuce inda wasu da dama suka rika karyatashi.
Idan ya wallafa Bidiyo akan rika rubuta masa 5M a comment kuma ya sha yin gargadin cewa baya so amma da yawa basu daina ba.
A yanzu dai yace ya janye waccan magana kuma kada a sakw masa maganar idan ba haka ba zai dauki mataki.