
Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami kenan a wannan Bidiyon tare da Dansa da matarsa suka koma gida a jirgin sama bayan da aka bayar da belinsu.
An ga mutane sun musu tarba ta karamchi ana ta tafi.
EFCC dai na zargin Malami da satar sama da Naira 8 sannan ta kwace kadarorinsa har guda 57 wanda darajarsu ta haura Naira Biliyan 200.
Kotu dai ta bayar da belin malami da dansa da matarsa akan Naira Miliyan 500 bayan sun sha zama a gidan yarin Kuje.