
UmmiKD wadda Bidiyon ta ya watsu sosai bayan rasuwar dan daban Kaduna, Habu Dan Damusa saboda kareshi da ta yi, a yanzu tace ta bude kofar Tuba, duk wanda yasan ya zageta ko ya ci mutuncin ta ya fito ya nemi gafara kuma zata yafe masa.
Saidai tace duk wanda bai nemi yafiyarta ba kasancewar Allah baya yafe laifin da akawa wani, to zasu hadu acan.
Saidai duk da haka, wasu ma ci gaba da zaginta suka yi.