
Sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin harin da ‘yan Kungiyar ÌŚWÀP suka so kai musu a sansanin Forward Operating Base (FOB) dake Mairari.
ÌŚWÀP sun so su afkawa sansanin sojojin da motoci 2 na yaki amma sojojin sun ankare dasu inda suka lalata duka motocin sannan suka jikkata tare da hallaqa wasu daga cikin maharan.
Nasarar ta samu ne bisa hadin gwiwar sojojin sama sana kasa.
Sannan daga baya sun bi daji inda suka ga gawarwakin ‘yan Kungiyar da kuma kwato makamai.