
Rahotanni sun bayyana cewa, malam Lawal Triumph ya kai Gwamnati kotu da kwamitin shura da hukumar ‘yansanda.
Yana nema ne a hanasu kamashi da gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin bàtàncì da ake masa na yiwa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
Saidai kotun ta ki amincewa da wannan bukata ta Lawal Triumph
Lauyan Gwamnati yace kotu ta yi watsi da bukatar ta malam Lawal Triumph inda tace za’a iya hukuntashi.