Friday, November 14
Shadow

Kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya, TCN yace ya samar da wuta me karfin da ba’a taba samun kamarta ba a Tarihin Najeriya

Kamfanin samar da wutar Lantarki na kasa, TCN ya bayyana cewa, ya samar da wutar lantarki me karfin 5,801 megawatts wanda a Tarihin Najeriya ba’a taba samun wutar lantarki me karfin hakan ba.

Saidai ‘yan Najeriya dake amfani da wutar sun musanta wannan ikirari inda suka ce basu gani a kasa ba dan kuwa yankuna da yawa na kasar na kwana cikin duhu.

A ranar Alhamis ne dai shugaban hukumar a fadar shugaban kasa dake Abuja ya tabbatar da hakan.

Yace sun samu wannan nasara ne a ranar 4 ga watan Maris.

Yace kuma rassan kamfanin wutar na jihohi sun tura wutar gaba daya zuwa ga ‘yan Najeriya.

Karanta Wannan  Likita ya gargadi masu amfani da man kara hasken fata inda ya bayyana munana cutukan da zasu iya kamasu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *