
A jiyane wakilan Gwamnatin Najeriyar suka je kasar Burkina Faso dan baiwa shugaba Ibrahim Traore Hakuri kan jirgin Najeriya da ya shiga kasar da sojoji 11 ba tare da izini ba.
Kalar Gaisuwar da suka yi da shugaba Traore ta dauki hankula sosai.
Saidai wasu ‘yan Najeriya sun rika mamakin wai hakuri kawai kasar ta Burkina Faso ke son Najeriya ta bata kamin a saki sojojin.
A jiyan dai an saki sojojin na Najeriya bayan ziyarar wakilan Najeriyar.
Wani abu da ya kara daukar hankalin mutane shine yanda wakilan suka shaidawa Gwamnatin kasar Burkina Faso cewa kalamai marasa dadi da wasu ‘yan Najeriya suka rika fadi akan kasar Burkina Faso ba da yawun Gwamnati bane.