
Adam A. Zango ya mayar da martani ga Abokin aikinsa, Tijjani Asase bayan da Tijjanin ya zargi Adamu da korar yaransa da kuma kin zuwa ya masa gaisuwar rasuwar mahaifansa.
Adamu yace lallai da gaske ya kori yaransa saboda a wancan lokacin za’a fito a zageshi amma yaranshi babu wanda zai fito ya kareshi.
Ya bayyana cewa game da rashin yiwa Tijjani Asase gaisuwar mahaifansa kuwa ya kirashi a waya kuma ya saka ta’aziyya a shafinsa na sada zumunta.
Yace dalilin kasa zuwa masa gaisuwar mahaifansa shine, a lokacin ana son a kamashi a Kano.