Friday, July 17
Shadow

Kalli Bidiyon: Kalli Yanda cacar bakin Adam A. Zango da Tijjani Asase ta kasance

Adam A. Zango ya mayar da martani ga Abokin aikinsa, Tijjani Asase bayan da Tijjanin ya zargi Adamu da korar yaransa da kuma kin zuwa ya masa gaisuwar rasuwar mahaifansa.

Adamu yace lallai da gaske ya kori yaransa saboda a wancan lokacin za’a fito a zageshi amma yaranshi babu wanda zai fito ya kareshi.

Ya bayyana cewa game da rashin yiwa Tijjani Asase gaisuwar mahaifansa kuwa ya kirashi a waya kuma ya saka ta’aziyya a shafinsa na sada zumunta.

Yace dalilin kasa zuwa masa gaisuwar mahaifansa shine, a lokacin ana son a kamashi a Kano.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Na koma gidan tsohon Mijina dana kasa hakuri nace sai ya sakeni, na iske ya auri wata matar wallahi ba zan boye ba na ji kishi da kewa sosai>>Inji Wannan bazawarar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *