
Gwamnan jihar Anambra Charles Soludo ya bayyana cewa, kaso 99.99 na masu laifuka da garkuwa da mutane da ake kamawa a jihar, Inyamurai ne ba Fulani ba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro dake gudana.
Hakan na zuwane a yayin da kusan duk wani laifi musamman na garkuwa da mutane da ya faru a yankin Inyamurai ana alakantashi da cewa Fulanine.
Lamarin dai ya jawo zazzafar Mahawara inda wasu ke cewa sun yadda wasu suka ce basu yadda ba.