
Tauraron Tiktok, Aminu J. Town ya bayyana cewa, maganar da Sadiq Sani Sadiq yayi ta bayar da shawara akan yanda za’a magance tsaro magana ce ta hauka.
Sadiq Sani Sadiq ya ce ya bayar da rayuwarsa sannan yana so shima dan shugaban kasa, Seyi Tinubu ya fito, Ministan tsaro, Christopher Musa shima ya fito, Malam Nuhu Ribadu shima ya fito a shiga daji.
Saidai J Town yace wannan maganace ta masu shaye-shaye da rashin wayau.
Saidai yace ba zai sake magana akan Sadiq Sani Sadiq ba.