
Wani malamin addinin Islama Bayerabe, Ahlussunah me suna Shaykh AbdulHakīm AbdurRaheem Al Kutubi ya bayyana cewa Bikin Eyo Festival na al’adun Yarbawa da shugaba Tinubu da matarsa Remi suka halarta shirkane.
Malamin yace musulmi bai kamata ya halacci wannan bikin ba.
Shugaba Tinubu bayan ya je Legas inda yake hutun Kirsimeti acan an ganshi a wajan Bikin Eyo Festival inda aka ganshi suna rawa shi da matarsa Remi.
Hutudole ya fahimci cewa, wannan bikin ana yinshi ne dan girmama wasu manyan mutane a kabilar yarbawa da suka mutu wanda har bauta musu ana yi, da kuma girmama masu sarautun gargajiya.