
Malamin Dariqa, Abulfatahi ya bayyana cewa, su ‘yan Dariqa, Garanti garesu wajan cikawa da Kalmar Shahada.
Ya bayyana hakane akan masu cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi bai cika da kalmar Shahada ba.
Yace dalili kuwa shine suna yin kalmar shahada safe da yamma.