
Tauraruwar fina-finan Hausa, Asma Wakili ta bayyana cewa, ta tuba ta daina yin Bidiyo babu dankwali.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyo data fito take sukar wani Bidiyo da ta gani yana yawo a kafafen sada zumunta na wata karamar yarinya da ke rawa a gidan Gala.
Tace duk da tasan itama tana aikata ba daidai ba amma kuma rawar da karamar yarinyar ta yi kuma ana ta shewa bai kamata ba.
Ta bayyana cewa Ta daina yin Bidiyo babu Dankwali amma Wando ne ba zata daina sakawa ba.