
Ganin diyar Ministan kasar Iran dake kula da tabbatar da saka Hijabi ta saka riga wadda babu kafada a wajan bikinta ya jawo cece-kuce.
Bayyanar Bidiyon a kafafen sada zumunta ya jawo zazzafar Muhawara wanda hakan yasa wasu ke sukar Gwamnatin da munafurci.
Shi dai wannan Ministan na kusa ne ga shugaban Jamhuriyar ta Iran.
Sunan Ministan Ali Shamkhani kuma a baya shine sakataren Ayatollah Khamenei sannan shine shugaban kula da tabbatar da saka Hijabi a kasar, kamar yanda daily Mail ta ruwaito.
A Bidiyon an ganshi tare da diyarsa inda sauran manyan baki a wajan ke musu tafi.
Ana dai ganin wannan shigartata ta yi kalar ta kasashen turai wadda kasar Iran ke yaki da irij Al’darsu.