
Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana cewa, shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba zai ci zabe ba a shekarar 2027.
Ya bayyana hakane a hirar da Jaridar Channels TV ta yi dashi.
Yace ko da a zaben 2023 Tinubu ba zabe yaci ba.
Yace yana da yakinin Tinubu ba zai ci zabe bane saboda yanda mutane ke cikin wahala a gwamnatinsa.