
Ana rade-radin cewa, wannan Bidiyon wa’azinne yasa kasar Saudiyya ta hana babban malamin Addinin Islama Sheikh Dr. Ahmad Gumi yin aikin Hajjin Bana.
A wa’azin dai, Sheikh Gumi ya soki kasashen Labarabawa bisa yanda suka baiwa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump makudan kudade amma suka saka ido ana kashe Falasdinawa.
Labarin hana Malam Aikin Hajji ya jawo cece-kuce sosai.