
Wannan ne wajan da aka ware a matsayin gurin da za’a binne gawar Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Ana dai jiran isar gawar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari zuwa Daura ne dan yi masa Sutura a yau.
Da misalin karfe 2 na ranane ake tsammanin Yin Jana’izar tsohon shugaban kasar.
Tuni manyan mutane irin su El-Rufai suka isa Daura suna jiran isar gawar Buhari.