Wani bidiyon kisan wulakanci da akawa wani bawan Allah ya tayar da hankula matuka inda aka ga an daure masa hannuwa an jefashi cikin Teku.
Rahotanni dai sun bayyana cewa kungiyar masu harkar kwayane suka kama wani daga cikinsu da ya musu laifi shine suka masa wannan mummunan hukunci.
Mutane da dama dai sun yi Allah wadai akan wannan inda da yawa suke cewa rashin Imanine.