
Kungiyar masu ikirarin Jìhàdì ta ÌŚWÀP sun wallafa wani Bidiyo wanda suka ce sun kaiwa wani sansanin sojojin Najeriya dake Mairari, jihar Borno hari ne.
Kungiyar ta wallafa Bidiyon inda aka ga mayakanta nata kabbara suna harbe-harbe.
A karshen Bidiyon an ga yanda suka wallafa motar sojojin da wasu makamai da suka kwace daga hannun sojojin
Zuwa yanzu dai Hukumomin soji na Najeriya basu ce koma ba kan lamarin.