
Malamin Addinin Islama, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa, akwai wata mata da mijinta ya saketa ya bata Naira Miliyan 7 da Mota amma tace bata so.
Malam ya kara da cewa, Matar tace ya taimaka ya roki mijinta ya mayar da ita ya karbi kudinsa da motar daya bata ita dai tana son ci gaba da zama dashi ta mutu a gidansa.
Malam ya bayyana hakane a daya daga cikin karatuttukan da yake yi.