
Wasu masu kwacen waya sun shiga gidan wata sabuwar Amarya a unguwar Gaida dake Kano.
Sun caccaka mata wuka sannan suka kwace mata waya, ta rika ihun barawo har mutane suka taru.
Barayin 3 ne inda jama’a da suka taru suka yi nasarar kama guda 2 daga ciki.
Amaryar dai an garzaya da ita Asibiti inda tana can tana samun sauki.