Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon yanda dansandan Najeriya ya harbe Dalibin dake kan hanyar zuwa rubuta WAEC ya mùtù

Ana zargin dansandan Najeriya da harbin dalibin dake kan hanyar zuwa rubuta jarabawar WAEC inda dalibin ya mutu.

Lamarin ya faru a jihar Oyo.

Mahaifin yaronne yake tuka mota inda yayi aron hannu sai aka yi rashin sa’a ya hadu da hukumar kula da hadurra ta jihar me suna, OYTMA.

Da aka tsayar dashi sai yaki tsayawa ashe ‘yansanda na kusa inda suka kara mai mota nan ma yaki tsayawa sai suka yi zuga suka bishi.

https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1925080799910490117?t=m8uYTW_Yg7509vo6kNenNw&s=19
https://twitter.com/OurFavOnlineDoc/status/1925080799910490117?t=m8uYTW_Yg7509vo6kNenNw&s=19

Anan ne daya daga cikin ‘yansandan yayi kokarin harbin tayar motar inda harsashin ya kuskure ya harbi dan me motar, Kehinde Alade me shekaru 14.

Karanta Wannan  Hotuna:Shugaba Tinubu ya gana da gwamnan Anambra, Charles Soludo

An garzaya dashi Asibiti inda acan ya rasu kuma an kai gawarsa mutuware dan ci gaba da bincike.

Kakakin ‘Yansandan jihar, Osifeso Adewale ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an kama dansandan da yayi harbin ana kan bincike kuma za’a sanar da jama’a sakamakon binciken.

Sannan yace an kai ‘yansanda na musamman wajan da abin ya faru dan tabbatar da tsaro.

Saidai a wani labari me kama da wannan da hutudole ke samu na cewa yanzu haka zanga-zanga ta barke a garin saboda wannan lamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *