
Bidiyon yanda wani dan sanda ya harbi tayar babbar motar jigila ta Luxurious Bus saboda direban motar yaki bashi cin hanci ya dauki hankula a kafafen sada zumunta.
Tayar motar dai ta fashe.
Saidai direban motar ya gitta motar a tsakiyar titi inda yace ba zai tafi ba sai dansandan ya sai masa sabuwar taya.