
A daren da ya gabata ne dai Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila suka tafi kasar Ingila dan tahowa da gawar Tsohon shugaban kasa, Marigayi, Muhammadu Buhari.
Shugaba Tinubu ne ya aike da su a matsayin wakilai.
A jiyane dai a hukumance aka sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar.
Gwamnan Katsina, Dikko Radda yace a garin Daura mahaifar Buhari yau za’a yi jana’izar tsohon shugaban kasar.