
Tauraron Tiktok, Idris Maiwushirya ya ci gaba da caccakar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha inda yake cewa ba zai taba yadda ya dakileshi ba.
Yace ba zai taba amincewa da hukuncin Abba El-Mustapha ba, saboda dan fim ne dan Nanaye.
Yace da alkaliyace ko Malam Aminu Ibrahim Daurawa suka masa hukunci zai iya yadda dashi amma ba zai taba amincewa da Hukuncin Abba El-Mustapha ba.
Yace ya tara kudi sama da Naira Miliyan 1 a Facebook amma saboda tsarewar da aka masa tasa ya kasa fiddosu har suka lalace.