Wednesday, November 19
Shadow

Kalli Bidiyon yanda Maiwushirya ya fita hayyacinsa, Yace Dubu 3 ce kawai ta rage a account dinsa, inda yace Abba El-Mustapha ya ja masa asarar Miliyoyin Naira

Tauraron Tiktok, Idris Maiwushirya ya ci gaba da caccakar shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El-Mustapha inda yake cewa ba zai taba yadda ya dakileshi ba.

Yace ba zai taba amincewa da hukuncin Abba El-Mustapha ba, saboda dan fim ne dan Nanaye.

Yace da alkaliyace ko Malam Aminu Ibrahim Daurawa suka masa hukunci zai iya yadda dashi amma ba zai taba amincewa da Hukuncin Abba El-Mustapha ba.

Yace ya tara kudi sama da Naira Miliyan 1 a Facebook amma saboda tsarewar da aka masa tasa ya kasa fiddosu har suka lalace.

https://www.tiktok.com/@maiwushiryabackup/video/7565605083686194439?_t=ZS-90sk7hvb50b&_r=1

Karanta Wannan  'Yan Kudu, Musamman Inyamurai na cewa, Kalaman rashin kyautawa da me magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga yayi akan Buhari tun kamin a Binneshi da sanin Tinubu yayi su, Hakan na zuwane duk da Bayo Onanuga ya goge kalam nasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *