Matar mutuminnan na kasar Equatorial Guinea da yayi lalata da matan aure sannan aka ga Bidiyon sama da 400 ta bayyana a bainar jama’a.
Matar dai itama an ga wasu Bidiyo da aka zargi tana lalata da wani wanda ba mijinta ba.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda da yawa suka bayyana cewa dama duk me yi sai an masa.
A wani sabon faifan Bidiyon da ya bayyana an ga matar tana rufe kanta saboda kunya yayin da take kokarin shiga kotu.
Ba dai a bayyana yaushe lamarin ya faru ba.