Wani magidanci me suna Anthony Nephew dan kimanin shekaru 46 dake zaune a Duluth, Minnesota ta kasar Amurka ya kashe kansa.
Lamarin ya farune da yammacin ranar Alhamis.
Hakanan an ruwaito cewa mutumin ya kashe matarsa me suna Kathryn Ramsland ‘yar kimanin shekaru 45 sannan ya kashe dansa me shekaru 7 me suna Oliver.
Mutumin wanda bashi da addini kamin kashe kansa ya bayyana cewa yana gudun irin yanda masu addini zasu rika kallonsa a matsayin shedan shi da iyalansa da kuma kakaba masa dokokin addininsu.
Mutane da yawa ne ke fama da matsalar tabin hankali a kasar Amurka.