
Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da Dauda Kahutu Rarara ya je Daura dan a masa nadin sarautar Sarkin Mawakan Hausa matasa a garin sun yi masa ruwan duwatsu.
Bidiyoyi na ta yawo a kafafen sada zumunta inda aka ga yanda matasa ke ta yaga fastar ta Rarara a Daura.
Rahotanni sun ce an yi ta jifarsa da tawagarsa da kyar suka sha.
A baya dai, Rarara ya yi baram-baram da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda dan Asalin Daura ne.