Monday, September 28
Shadow

‘Yan gida daya su 5 sun mùtù bayan cin Abinci me guba

Wasu ‘yan gida daya su 5 sun mutu bayan cin abinci me guba a garin Ogidi, dake karamar hukumar Idemili North ta jihar Anambra.

Mahaifiyar su ma na can kwance rai hannun Allah a Asibiti.

Lamarin ya faru ranar Asabar 3 ga watan Mayu 2025 kuma ya jefa mutanen garin cikin damuwa.

Mahaifin yaran Pa Robinson Aghalu dan shekaru 76 wanda tsohon soja ne yace yaran nasa sun fara amai da ciwon ciki ne bayan cin abincin da mahaifiyarsu ta dafa.

Su 6 ne suka ci abincin kuma guda 5 sun mutu.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Tochukwu Ikenga ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace sun dauki abincin dan zuwa a yi gwaji.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo da hotuna yanda mayakan Kungiyar ÌPÒB dake son kafa kasar Bìàfrà suka kashe sojojin Najeriya 2 kuma suka kwace kayan aikin sojojin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *