
Rahotanni daga legas na cewa, hukumar sojojin sama sun kai farmaki ofishin hukumar wuta ta jihar, Ikeja Electric inda suka ci zarafin ma’aikatan hukumar ciki hadda shugabar ma’aikatar.
Lamarin ya farune bayan da Hukumar sojin sama dake barikin Sam Ethan Base aka dauke musu wuta saboda kasa biyan bashin sa ake binsu.
Bidiyo da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta ya nuna yanda sojojin suka ci zarafin wasu ma’aikatan hukumar.
Shugabar ma’aikatar, Folake Soeten tace sun kamata sun kulleta a cikin but din mota a yayin cin zarafin.
Saidai hukumar sojin saman na kokarin cewa bata san wane sojoji ne suka je suka aikata wannan lamari ba.
Saidai dan jarida, Oseni Rufai ya bayyana cewa, karyane hukumar sojojin saman tace bata san wadanne sojoji ne suka je suka aikata wannan lamari ba.
Yace akwai takarda da wani kwamandan sojojin yayi barazanar daukar mataki akan hukumar wutar.
A wata hira da aka yi da daya daga cikin ma’aikatan hukumar wutar ta IKEJA Electric yace da sojojin suka je sun kwace musu wayoyi sannan kuma sun lalata musu kyamarori.
A wata majiyar ma an ce sojojin har wasu kaya suka kwasa suka tafi dasu sannan sun lalata wasu kayan aikin kamfanin.