
Wani mutum ya kutsa tsakanin jami’an tsaro ya kama Nonuwan shugabar kasar Mexico, Claudia Sheinbaum a wajan wani taro ranar Talata.
Sannan yayi yunkurin sumbatarta amma jami’an tsaro suka kai kansa suka hanashi.
An dai kamashi sannan shugabar kasar tace zata tabbatar ta nemi hakkinta kan cin zarafin da ya mata.
Tace zata nemi hakkin nata ne musamman saboda ya zama izina ga sauran masu yunkurin cin zarafin mata.