Wednesday, April 29
Shadow

Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Minista da cewa ya rufawa kansa Asiri kada yayi magana akan Trump

Kakakin majalisar Dattijai Sanata Godswill Akpabio ya gargadi Kingsley Udeh (SAN) da cewa, kada ya sake ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirkaz Donald Trump.

Ya bayyana masa hakane ranar Alhamis yayin tantance shi dan bashi ministan kimiyya da Fasaha.

Bayan da Kingsley Udeh (SAN) ya gabatar da kansa a gaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya bayar da damar a masa tambayoyi amma ya gargadeshi da cewa, kada ya amsa tambaya akan shugaban kasar Amirka, Donald Trump.

A karshe dai majalisar ta amince da nadin Kingsley a matsayin Ministan.

Shidai Godswill Akpabio a baya yace bai isa ya baiwa Trump amsa ba sai abinda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yace.

Karanta Wannan  Ni da kaina na je ofishin EFCC ba kama ni akai ba>> Inji Tsohon Me kula da kudi na kamfanin mai na kasa, NNPCL, Umar Ajiya Isa da ake zargi da satar Dala Biliyan $7.2 na gyaran matatun man fetur din Najeriya

trump dai na barazanar kawo Khari Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *