
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta kama wani mutum da me suna Mbala Dajou Abuba a filin sauka da tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano dake Kano yana shirin fita da kwayoyi zuwa kasashen waje.
An kama mutumin da ya hadiyi kullun Hodar Iblis da yawa yana shirin fita da ita zuwa Istanbul babban birnin kasar Turkiyya.
Mutumin dan asalin Zaire ne ta kasar Angola kuma an kamashine ranar Talata, February 25, 2025 inda yake shirin hawa jirgin sama zuwa kasar Egypt wanda daga can zai wuce zuwa kasar Turkiyya.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa mutumin yace yana aikin kai sakonnine a kasarsa ta Angola kamin ya fada harkar safarar kwaya.