Monday, March 24
Shadow

Hisba ta kama matasan da ba sa yin azumi da masu askin banza a Kano

Jami’an Hukumar Hisba a jihar Kano sun kama wasu matasa gandaye da ake zargi da kin yin azumi a ranar farko ta watan Ramadan.

Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Abubakar ne ya tabbatar da kamen ga manema labarai a jihar.

Ya kara da cewa an kama matasan ne yayin sintiri da jami’an hukumar ke yi a sassa daban-daban na birnin Kano.

Haka kuma, hukumar ta cafke kimanin mutane 60 da ke da askin banza, wanda ya sabawa dokokin shari’a da al’adun gari.

Bugu da kari, Hisba ta kama wasu direbobin baburan adaidaita sahu (keke napep) da ake zargi da cakuda maza da mata a baburansu, lamarin da hukumar tace ba za ta lamunta da shi ba.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna da Bidiyo sun bayyana na wannan dan kasuwar yana lalata da matan manyan mutane

Hukumar ta Hisba ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da sintiri don tabbatar da bin dokokin shari’a a cikin watan Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *