
Bidiyon dan shugaban kasa, Seyi Tinubu yana gaiwa da diyar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari sannan ya sumbaci daya ya jawo cece-kuce sosai.
A Bidiyon, an ga Yusuf Buhari a zaune inda Seyi ya Mikawa Zahara Buhari hannu suka gaisa sannan ya zagaya ya sumbaci ‘yar uwarta.
Lamarin dai ya jawo zazzafar Muhawara inda wasu ke cewa masu kudi ba ruwansu da haramun wajan gaisawa da mata.