Wata cuta da aka kira da Ring worms dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana.
Cutar dai wadda irintace a karin farko da aka gani a jikin dan adam ta bayyana ne a jikin wani dan kasar Amurka.
Mutumin dai dan Luwadi ne wanda kuma yaje kasashe daban-daban yayi lalata da maza masu yawa.
Bayan da ya koma kasarsa ta Amurka ne sai aka ganshi da wannan cuta.
Saidai masana kimiyyar lafiya sun ce kada mutane su tayar da hankali dan cutar bata kai matakin barazana ga sauran al’umma ba.
Ko da dai cutar Kanjamau akwai wasu majiyoyi dake cewa daga wajan ‘yan Luwadi aka fara samota, hakanan ta tabbata cewa masu Luwadi sun fi saurin kamuwa da cutar.