‘Yansanda a jihar Imo sun kama wannan matar me suna Oluchi Nzemechi, ‘yar Kimanin shekaru 27 dake zaune a Uzoagba karamar hukumar Ikeduru ta jihar bayan data kashe mijinta.
Matar ta amsa laifinta ba tare da matsala ba.
Tace mijinta dan amfarar yana gizo ne kuma itama ya koya mata.
Tace sun damfari wani dan kasar Indonesia kudin kasar har Naira Miliyan 250 amma ta yi ta fama da mijinta ya bata kasonta amma yaki shine ta yi amfani da wukar dakin girki ta kasheshi.
Tace da farko ta yi rubutu na cewa wanine ya kasheshi har ma yana son yanzu kuma ya koma kan iyalansa ta dora takardar akan gawarsa ta tsere amma duk da haka sai da asirinta ya tonu.
Mijin nata dai sunansa Kelechi Nzemechi dan kimanin shekaru 31.
Kakakin ‘yansandan jihar, ASP Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace ana kan bincike kuma idan aka kammala za’a gurfanar da me laifin a kotu, kuma yace suna kokarin kwato kudin da aka yi damfarar dan mayarwa mesu.