Saturday, April 26
Shadow

Kalli Hoton mutumin da ya sa-yar da ‘ya’yan cikinsa har guda 6 a jihar Sokoto

An kama wannan mutumin me suna Malam Bala Abubakar a jihar Sokoto bayan samunaa da laifin sayar da yara har guda 28.

Wani abin mamaki ma shine cikin yaran da ya sayar hadda ‘ya’yansa guda 6.

An dai yadda da Malam Bala Abubakar a matsayin me kula da marayu.

Hukumar ‘yansanda ta jihar Sokoto tace yana sayar da yaranne ga wasu mata Elizabeth Oja da Kulu Dogonyaro da sunan za’a kai yaran Abuja dan wani mutum ya rika basu kulawa me kyau.

Malam Bala dai yana zaunene a unguwar Tudun Wada dake jihar Sokoto.

Kuma wanda suka sanshi sun yi mamakin abinda ya aikata.

Karanta Wannan  Sadiya Haruna Ta Grime Ni, Shekaru Na 35 Ita Kuma Shekarunta 48, Kuma Kafin Mu Rabu Na Ba Ta Hakuri Ya Fi Sau Milyan Duk Da Cewa Ita Ta Yi Min Laifi, Saboda Na Kama Ta Tana Cin Abinci Da Wani Gardi Da Muharraminta Ba, Cewar G-Fresh Al'Amin

Lamarin dai yana hannun ‘yansanda inda ake ci gaba da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *