Tuesday, January 28
Shadow

Kalli Hotuna: Kwamandan Sojojin Najariya da aka kkashe tare da Wasu sojoji sama da 20 a jihar Borno

Kwamandan sojojin Najariya na runduna na 149 dake Malam Fatori jihar Borno Lt. Col. TE Alari da aka kashe kenan a ranar 24 ga watan Janairu a wani mummunan hari da ya faru.

An kashe shine tare da wasu manyan sojoji 2 da kuma sauran kananan sojoji 17.

Ana zargin kungiyar B0k0 Hàràm da ISWAP ne suka kai harin.

Saidai rahotanni sun banbanta kan yanda aka kai harin.

Inda kafafen yada labarai da yawa sukace an kai harinne kan sansanin sojojin dake garin Malam Fatori dake iyakar Najeriya da Nijar, a bangare guda kuma, shahararren me watsa labarai na tsaro, Zagazola Makama ya ruwaito cewa harin kunar bakin wakene aka kai kan tawagar kwamandan.

Karanta Wannan  Na ga yanda Manya a gidan yari ke yin Lùwàdì da Kananan yara

Saidai abu daya daya tabbata shine an kai harin kuma an kashe sojojin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *