Monday, December 16
Shadow

Kalli Hotuna: Matashiya ta hau gini me tsawo ta fado ta mùtù bayan da aka hanata shigar banza a kasar Iràn

Wata matashiya ‘yar kasar Afghanistan da ke karatu a jami’ar kasar Iran ta hau saman gini me tsawo ta fado ta mutu bayan da aka hanata yin shigar banza.

Matashiyar dai me suna Arezo Khavari ‘yar Kimanin shekaru 16 tana da son saka wando saidai jami’an da’a na Iran sun hanata sawa, sannan bata son saka dankwali inda aka ce mata idan dai ba zata rika saka dankwali ba za’a koreta daga makarantar.

Abokan ta dai sun ce barazanar korar ta daga makarantar ya daga mata hankali sosai inda ta yi ta amai.

Babanta yace ta sameshi hankalinta a tashe inda ta rika gaya mai cewa,ya tayata da addu’a Allah yasa kada a koreta daga makarantar.

Karanta Wannan  Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Hakanan abokanta sunce a baya makarantar ta rika takurawa dalibar inda ake mata fada saboda ta cika wasa da yawan dariya da yawan abokai.

A ranar da lamarin zai faru dai matashiyar ta bar makaranta ba tare da izini ba.

An kira iyayenta aka gaya musu inda suka bazama nemanta, daga baya aka gano gawarta ta hau sama ta fado.

Mahaifin nata dai wanda direban motane ya kai kara wajan ‘yansanda amma kasancewarsa dan kasar Afghanistan, ba lallai a dauki wani mataki ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *