Tuesday, May 13
Shadow

Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi ‘yan NNPP da suka koma APC

Shugaban jam’iyyar APC na Kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya karbi jiga-jigan jam’iyyar NNPP wadanda su ka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Mashawarci na musamman ga Dr. Ganduje, Aminu Dahiru ne ya wallafa hotunan yadda tarbar ta kasance.

Ganduje bayan karbar sabbin ‘yan APC din ya bayyana cewa sun lashe zaben shekarar 2027 sun gama.

Ya bayyana cewa akwai karin Gwamnoni da manyan ‘yan siyasa da zasu shiga jam’iyyar tasu.

Daga cikin wadanda Abdullahi Umar Ganduje ya karba sun hada da Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila da dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Kibiya/Bunkure, Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kano Dr. Baffa Bichi da tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Danbatta Makoda, Hon. Badamasi Ayuba

Karanta Wannan  Akwai yiyuwar shugaba Tinubu yayiwa majalisar zartarwa garambawul

Sauran sun hada da Hon. Abdullahi Sani Rogo da Rt. Hon. Zubairu Hamza Masu da Hon. Muhammad Diggol da Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada da Hon. Abbas Sani Abbas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *