
Kasar Indonesia ta zane wasu mutane maza 2 da aka kama suna aikata Luwadi.
an zane su ne a gaban gwamman Mutane dan ya zama izina ga meyi ya daina.
An yi wannan bulala ne a yankin Aceh na kasar a ranar Alhamis. Shi wannan yanki na Aceh ya kasance yana aiki ne da shari’ar Musulunci.
Tun a watan Nuwamba da ya gabata ne mutane suka kamasu turmi da tabarya wanda daga nan ne suka kaisu kotun shari’ar Musulunci.