
Shugaban ‘yan Bindiga me suna Kachalla Bugaje ya bayyana a baya cewa, ya tuba daga yin garkuwa da mutane inda yace mutane guda 50 da yayi garkuwa dasu, ya sakesu ba tare da karbar kudin fansa ba.
Bayan nan ne kuma aka ganshi yana jagorantar mayakansa suna zikiri da salatin Annabi.
Bugaje ya bayyana nadama sosai bisa abinda ya aikata tare da jawo hankalin sauran shuwagabannin ‘yan Bindiga da su ajiye makamansu su koma ga Allah.
Ganin bidiyon har yanzu da makamai a hannunsu shi da yaransa yasa da yawa suke zargin cewa ba da gaske yake maganar ajiye makaman ya daina yaki ba.