
A jiyane dai Hukumar Hisbah ta Kano ta saka Haramcin jin wakar Hamisu Breaker ta Amanata saboda a cewarsu tana karfafa yin zina.
Saidai duk da wannan haramcin, bai hana mutane ci gaba da sauraren wakar ba, kamar ma an ce a ci gaba da saurarene.
A daya daga cikin Bidiyon an ji wata na cewa yanzu suka fara sauraron wakar.
Da alama dai daukakar da wakar ta samu bayan maganar Hizbah ko kamin haramcin bata sameshi ba.