
Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Nuhu ta fito ta bayyana dalilin da yasa ta fada wahalar rayuwar da aka ganta a ciki ake ta cece-kuce bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi da ita.
Ummi Nuhu a sabuwar hirar ta da Hadiza Gaon ta bayyana cewa, Babban Kuskuren da ta aikata shine a lokacin data samu dama, bata yiwa kanta tanadin komai ba, jin dadin rayuwa akai ta yi.
Tace amma tana fatan jarumai mata musamman masu tasowa a yanzu zasu dauki darasi daga Rayuwarta.
Ummi Ta kuma bayyana sunayen jarumai mata da suka bata kudi.
Daga ciki tace akwai Momi Gombe da Fatima Kinal da sauransu.
Daga karshe ta nuna farin ciki kan soyayyar da aka nuna mata.