
A dasu da safene aka ga Bidiyon Alhassan Ado Doguwa yana kwambo a kan titin Birnin Landan na kasar Ingila.
Lamarin ya jawo cece-kuce inda mutane sukai ta mamakin dan majalisar Tarayya guda da nuna irin wannan halayya.
Saidai ashe kallo be kare ba, a karo na biyu an ga Doguwa yana daukar hoton a cikin dakin Otal dib da ya sauka inda a wannan karin har abinci yaci a cikin bandaki.